![]() |
| Usman Al-amin(PhD) |
Wasu matasa a Nguru sun bayyana cewa suna nan suna shirin kafa wata kungiya da zata wayar wa jama'ar garin kai dangane da alherin Dr. Usman Al-amin idan ya zama Provost.
A zantawarsu da wannan Dandali a ranar Lahadi a Nguru, matasan suka ce za su bi lungu da sako-sako na garin da kewaye domin nuna nagartar Daktan idan aka ce ya zama Provost.
Wani matashi mai suna Umar da ya yi magana a madadin sauran, ya tabbatar da cewa shirye-shiryensu ya yi nisa domin ganin kungiyar ta tabbata.
Ya ce a kungiyance za su bi masu ruwa da tsaki a koina a fadin jihar domin neman goyon bayansu kan Al-amin Usman ya kasance shugaban Kwalejin Atiku Abubakar mai zuwa.
Yana mai cewa idan Daktan ya sami matsayin to babu ko shakka dalibai da iyalansu za su sami sa'ida.
A ' yan kwanakin nan jama'a da dama ne ke ta kiraye-kirayen Daktan da ya naimi shugabancin Kwalejin Atiku Abubakar dake Nguru, to sai dai har kawo yanzun hakar Dandalin ba ta cimma ruwa ba a kokarinsa na jin martanin Daktan kan wannan batu.
Dr. Usman Al-amin wanda a halin yanzu ke daf da kammala karatunsa na Digirin digirgir a Jami'ar birnin Hamburg na kasar Jamus, malami ne a sashen Tarihi a Jami'ar Maidugurin jihar Borno.

No comments:
Post a Comment