Thursday, April 25, 2019

DALIBAN Dr. AL-AMIN SUN KOKA GAME DA YANKEWAR HOTUNANSA A KAFAR SADA ZUMUNTA

Dr. Usman Al-amin

Wasu tsoffin daliban Dr. Usman Al-amin da suka ce Daktan ya koyar da su, sun koka kan abin da suka kira daina ganin fatan alheri wa Daktan na 'yan kwanaki a kafafen sada zumunta.

A zantawarsu da wannan Dandali a ranar Alhamis a Nguru, daliban suka ce suna jin dadin yadda ake danganta Al-amin da shugabancin Kwalejin Atiku Abubakar dake Nguru.

Suka ce suna kuma jin dadin yadda suke ta ganin hotunan Daktan mabambanta a kafar suna yawo abin da a cewarsu yakan sa su su rika tuna alheransa da ya shuka musu.

Wani tsohon dalibinsa da ya ce sunansa Musa ya ce Dr. Usman Al-amin ya koyar masa kuma ya taimaka masa sosai a lokacin da yake koyo.

Dalibin ya ce yana jin dadin yadda ake danganta Al-amin da neman Provost domin a ganinsa Daktan zai taimaka wa dalibai matuka.

Shi ma wani tsohon dalibinsa a Kwalejin ta Atiku Abubakar wanda ya ce wanda ya ce a boye sunansa ya tabbatar wa wannan Dandali cewa, Dr. Al-amin mutumin kirki ne ba zai tsauwala wa dalibai da iyalansu ba matuka.

Ya ce tabbatas idan Dr. Al-amin ya sami Provost to fa kakar dalibai ta yanke saka kasancewarsa mai tausayi da ba sira da taimako.

A dan tsakanin nan ne dai aka sami bullar wasu sakonni a kafafen sada zumunta, musamman na Facebook wadanda a cikinsu ake yi fatan ya sami Provost, kafin a sami tsagaitawarsu a kafar cikin 'yan kwanakin nan.

Iyaye da 'yan uwa da aminan ne suka yi ta kiraye-kirayen, to sai dai har kawo yanzun hakar Dandalin ba ta cimma ruwa ba a kokarinsa na jin martanin Daktan kan wannan batu.

Dr. Usman Al-amin wanda a halin yanzu ke daf da kammala karatunsa na Digirin digirgir a Jami'ar birnin Hamburg na kasar Jamus, malami ne a sashen Tarihi a Jami'ar Maidugurin jihar Borno.

No comments:

Post a Comment