Friday, April 05, 2019

Da za a bukaci ji daga garemu to da mun goyi bayan Dr. Al-amin a Provost— Wasu daliban AACOLIS Nguru

Dr. Usman Al-amin

Wasu dalibai a Kwalejin Atiku Abubakar dake Nguru sun bayyana cewa za su goyi bayan Dr. Al'amin a neman shugabancin makarantarsu muddun aka saurari ra'ayinsu.

A zantawarsu da wannan Dandali a ranar Juma'a a garin Nguru, daliban suka ce a yanzu ba za su ce komai kan dalilansu na cewa za su iya goyon bayan Daktan duba da cewa su daliban Makarantar ne a halin yanzun.

Wani dalibi da ya ce a boye sunansa ya tabbatar wa wakilin  wannan Dandali cewa a yanzu dai ba zai kara cewa komai ba, kasancewar shi dalibi ne, to amma sai dai ya ce tun lokacin da ya lura ana neman Dr. Usman Al-amin da nemi shugabancin Kwalejin sai ya sa a ransa cewa an yi kyakkyawan zabi.

Dalibin ya kuma kirayi Daktan Al-amin da amsa kiran jama'a domin ya dora makarantarsu kan gwadabe nagari wanda basirarsa ta hango.

Ya ce Dr. Usman Al-amin ya karantarwa wata yayarsa inda yake jin yadda 'yar uwarsa take yaba Daktan kan kokarinsa na ganin ya ciyar da dalibai gaba.

Shi ma dai wani dalibin makarantar dake shekarar karshe da ya zanta da wannan Dandali ta kafar WhatsApp ya nuna fatan alherinsa ne ga Dr. Usman Al-amin a matsayin Provost.

Ya ce Dr. Usman Al-amin ya cancanta duk kuwa da ba zai iya yin karin haske a lokacin kan cancantar ba.

Dalibin ya kuma sake yin kira ga Dr. Al-amin Usman da ya amsa kiran jama'a, yana mai nusar da shi cewa ya kamata Daktan ya fifita son jama'a ba wai son kansa ba.

A 'yan makwannin nan dai kiraye-kiraye kan Daktan da ya amsa kiran jama'a kan batun shugabancin Kwalejin ya yawaita, to sai dai har kawo yanzun hakar Dandalin ba ta cimma ruwa ba a kokarinsa na jin martanin Daktan kan batun.

Dr. Usman Al-amin wanda a halin yanzu ke daf da kammala karatunsa na Digirin digirgir a Jami'ar birnin Hamburg na kasar Jamus, malami ne a sashen Tarihi a Jami'ar Maidugurin jihar Borno. 

No comments:

Post a Comment