Monday, April 01, 2019

DA DUMI-DUMI: Daliban Nguru a manyan makarantu za su gudanar da addu-o-in Dr. Al-amin sai ya yi Provost


Wasu dalibai 'yan asalin karamar hukumar Nguru dake a manyan makarantu sun bayyana cewa za su gudanar da jerin addu-o-i na musamman domin ganin Dr. Usman Al-amin ya yi Provost.

Daliban a zantawarsu da wannan Dandali a Jami'ar Bayero Kano, a ranar Lahadi suka ce suna jaddada goyon bayansu ga Dr. Usman Al-amin a Provost, tare da nuna shirinsu na gudanar da addu-o-i na musamman domin ganin cewa sai Daktan ya yi Provost.

Jama'a da dama ne dai ciki da wajen Nguru ke ta yin kiraye-kiraye ga Daktan da ya zo ya jagororanci Kwalejin Atiku Abubakar dake Nguru a fatansu na alheri da suke yi masa.

Idan za a iya tunawa ko a Asabar din da ta gabata ma sai da wasu mutane a Nguru suka yi irin wannan kiran, to amma har kawo yanzu ba mu iya jin martanin Daktan kan wannan batu ba.

Daktan Usman Al-amin dai Malami ne a tsangayar Tarihi a Jami'ar Maidugurin jihar Borno, wanda a halin yanzu ke daf da kammala karatunsa na Digirin digirgir a Jami'ar birnin Humbug na kasar Jamus.

No comments:

Post a Comment