Sunday, March 31, 2019

An kirayi Dr. Al-amin da ya naimi Provost


Jama'a da dama ne a garin Nguru suka bukaci Dr. Usman Al'amin da ya mika kokon bararsa na naiman shugabancin Kwalejin Atiku Abubakar Nguru da aka fi sani da sunan Legal.

Wasu da suka zanta da wannan Dandali a Nguru sun nuna cewa suna yi wa Daktan fatan alheri a zama Provost.

Wani magidanci a Nguru ya ce ya san Dr. Al'amin jajirtacce ne tun a kuruciya.

Ya ce mutum ne mai kokarin gaske ta fuskar karatu da riko da addini da kuma martaba kowa.

"Lallai ya kamata a jaraba shi domin shi ma zai yi iya kokarinsa wajen habakar Makarantar" a cewarsa.

Ita ma dai wata mata da ta ce malamar Makaranta ce a zantawarta da wannan Dandali ta wayar salula a ranar Asabar ta fada cewa, da a ce za ta yi ido hudu da Dr. Usman Al'amin, to da sai ta ba  shi shawarar ya naimi Provost.

Dandalin ya yi kokarin jin martanin Daktan wanda a halin yanzu ke can a birnin Humbug na sakar Jamus inda yake karatunsa na Digirin digirgir a jami'ar birnin, to amma sai dai hakar Dandalin ba ta cimma ruwa ba.

Dr. Usman Al'amin dai Malami ne a tsangayar Tarihi a Jami'ar Maidugurin jihar Borno.

No comments:

Post a Comment