Wednesday, September 30, 2020

DAN MAJALISA DAYA NA PDP A JIHAR YOBE YA KOMA JAM'IYYAR APC


Dan majalisar jiha na jam'iyyar PDP mai wakiltar Nguru ta tsakiya a jihar Yobe, Hon. Lawan Sani Inuwa, ya fice daga jam'iyyar inda ya koma jam'iyyar APC.

A Larabar nan ce dai labarin sauya shekar da hotunan dan majalisar ya game dandalin sada zumunta na galibin wadanda yake wakilta.

Batun sauya shekar Hon. Lawan Sani ya janyo cecekuce a Nguru, inda wasu ke ganin cewa sauyin shekar babu abin da za ta janyo wa dan majalisar face nadama, yayin da wasu ke ganin sauyin shekar shi ya dace.

Wani dan jam'iyyar PDP mai goyon bayan dan majalisar da ya bukaci a boye sunansa ya shaida wa wannan dandali cewa Hon. Lawan bai yi aiki da shawara ba a yayin sauyin shekarsa.

To sai dai a zantawarsa da wannan dandali a daren Larabar nan Hon. Lawan ya kwatanta sauya shekarsa da sinadarin gaskata mafarkin wadanda ake wakilta.

Hon. Lawan ya kara da cewa duk fadi-tashinsa a tsohuwar jam'iyyarsa da kuma sabuwa da ya koma shi ne domin ya ga ya cimma muradun al'umarsa gaba daya kwata.

Ya ci gaba da cewa bai fice daga jam'iyyar PDP ba zuwa APC, har sai da ya nemi shawarwari daga masana kan alheri yin hakan ko akasin haka ga mutanensa.

Ana sa ran daga gobe Alhamis ne zuwa wani lokaci za a gudanar da gangamin wankar dan majalisar a Nguru.

Da ma dai Hon. Lawan dan jam'iyyar APC ne Kafin daga bisani ya koma PDP.

Abin jira a gani dai a halin yanzu shi ne martanin jam'iyyar PDP kan sauyin shekar, tare sauraran ganin shin ko Honarabil din ya koma APC ne tare da Jama'arsa ko kuma dai shi kadai ya koma?

No comments:

Post a Comment