Sunday, November 27, 2016

ANWARUL ISLAM NGURU: Bikin maraba da sabbin dalibai 2016

Bikin tarbar dalibai 2016



Makarantar Sakandaren Anwarul Islam Nguru ta gudanar da bikin marhabin ga sabbin daliban da ta dauka wannan shekarar (2016).

An gudanar da bikin ne a safiyar Lahadin nan a harabar makaratar dake unguwar Bulabulin Nguru.

Mutane da dama ne suka gabatar da jawabai daban-daban a wurin bikin.

A jawabinsa na marhabin da ya gabatar a wurin bikin, shugaban makarantar Malam Kabir Ali, ya ja hankulan daliban ne akan muhimmancin ilimi da kuma nemansa.

Malam Kabir Ali ya ce neman ilimi sai an daure kuma rago ba ya iya neman ilimi.

Daga nan sai ya bukaci daliban da su zama masu hakuri da halayya tagari don su bambanta da wadanda ba sa makaranta.

Shi ma dai a nasa jawabin, shugaban malamai na makarantar Malam Muhd Baba Nguru, muhimmancin ilimin da nemansa ya nuna, inda ya kawo ayoyi daga cikin Alkur'ani mai girma, da Hadisan manzon Allah (S.A.W) da suke nuna muhimmancin nema da falalar ilimi.

Ya kuma tsawatar wa daliban da su kauce wa aikata duk wata mummunar dabi'a  a ciki da wajen makaranta.

Yana mai nuna musu muhimmanci da tasirin shaidar sakandare a rayuwar neman ilimi ga baki daya.

Shi ma dai Malam Muhd Ibrahim Ahmad wanda ke zama mai shiga tsakani a makarantar ya gabatar da jawabinsa ne kan ilimi da wajabcin nemansa ga al'umar musulmai ga baki daya.

Bikin dake zama na farko a tarihin makarantar, ya sami halartar mutane da dama da suka kunshi malaman makarantar da dalibai da sauran jama'ar gari.

No comments:

Post a Comment