Dan majalisa mai wakiltar Nguru ta tsakiya Hon. Lawan Sani ya tabbatar wa mata a mazabarsa cewa ya shirya tsaf domin fara raba musu jari kamar yadda ya alkawuranta musu a lokacin yakin neman zabe.
Hon. Lawan wanda ke a birnin Abuja a halin yanzu ya fada a zantawarsa da wannan Dandali ta wayar salula cewa zai fara ba wa matan jarin ne da ya dawo Nguru.
To sai dai Honarabil din ya kokwanta cewa balalle ne dukkannin alkawaran su samu ba, inda ya buga misali da wasu gaggan shugabanni da su ma ba su iya cika dukkan komai ba.
Ya ce Allah shi ke cika komai daidai, to amma ya ce zai yi iya kokarinsa wajen ganin Allah ya taimake shi ya cika su gaba daya.
Ko da wakilin Dandalin tambaye shi shin ko mai zai ce game da zargin da mutum 10 ya koma APC? Nan take sai ya karyata zargin cikin raha, inda ya ce ko a ahalin gidansu ma wadanda ya koma da su sun fi mutane 10.
A doguwar hirarsa da wannan Dandali Hon. Lawan ya kuma yi kakkausan martani ga masu cewa sai da ya danke wasu 'yan sulalla kafin sauyin shekarsa, inda ya kalubalanci duk wani mai ikirarin hakan akan ya kawo hujja.
Yana mai tabbatar da cewa ya koma APC ne ba tare da ya gindaya ko an gindaya masa wani sharadi ba.
Wakilin wannan Dandali ya sake tambayar sa game da zargin rashin yin shawara da 'yan tsohuwar jam'iyyarsa gabanin sauyin shekarsa? Hon. Lawan sai ya kada baki ya ce, ko kadan bai yi gaban kansa ba har sai da ya naimi shawara.
Ya ce wadanda ya shawarta sun san ya yi Shawara, wadanda kuma neman bai kai gare su ba, ya ce to ka ga wadannan dole su ba a yi shawara ba kwata-kwata.
Hon. Lawan daga karshe ya gode wa masoyansa da ma daukacin al'umar Nguru, inda ya musu albishirin cewa akwai wani gagarumin gangami da za a shirya na neman gaisuwa.
Sannan kuma ya yi barazanar neman hakkinsa daga duk wanda ya yi masa yarfe ko kazafin bai ji ba bai gani ba.